BAMBANCI DA KAMANCE TSAKANIN MIYAR GARGAJIYA DA TA ZAMANI

BAMBANCI DA KAMANCE TSAKANIN MIYAR GARGAJIYA DA TA ZAMANI

  • The Complete Research Material is averagely 62 pages long and it is in Ms Word Format, it has 1-5 Chapters.
  • Major Attributes are Abstract, All Chapters, Figures, Appendix, References.
  • Study Level: BTech, BSc, BEng, BA, HND, ND or NCE.
  • Full Access Fee: ₦6,000

Get the complete project » Instant Download Active

BABI NA XAYA

1.0      GABATARWA

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah maxaukakin sarki wanda ya halicci mutum da aljan, ya kuma yi wa xan Adam baiwa wadda bai yi wa sauran halittunsa ba wato ya hore masa harshe domin sadarwa. Wannan aikin zai yi tsokaci ne a kan bambanci da kamance tsakanin miyar gargajiya da ta zamani. Don haka na sanya wa wannan aikin nawa suna “Bambanci da kamance tsakanin miyar gargajiya da ta zamani.”

Bugu da qari, na yi qoqarin karkasa wannan aikin har zuwa babi huxu (4). A babi na farko na yi qoqarin gabatar da littafin, abin da Hausawa ke kira waiwaye adon tafiya, wato bitar ayyukkan da suka gabata. Na kalli wasu ayyukkan da Magabata suka yi a kan sana’o'in Hausawa domin ganin inda suka tsaya da kuma dacewa da ci gaba da wannan bincike. Bayan wannan kuma, na yi qoqarin nuna hanyoyin da wannan aikin nawa ya bi domin samun haske na ci gaba da bincike. Daga nan kuma sai muhallin bincike wato iyakokin da wannan bincike zai tsaya, sai kuma muhimmancin bincike duk domin ganin kwalliya ta biya kuxin sabulu.

8


A babi na biyu na yi qoqarin kawo ma’anar miya, da kuma kayayyakin da ake amfani da su wajen haxa miyar gargajiya da ta zamani. Na uku na yi qoqarin kawo bayani a kan yadda ake dafa miyar gargajiya da ta zamani, a nan ne na yi qoqarin nuna bambanci da kamance tsakanin miyar gargajiya da ta zamani.

A babi na huxu na kawo canje-canjen da ake samu tsakanin miyar gargajiya da ta zamani kuma a nan ne na kammala aikin nawa ta kawo irin bambanci da kammance tsakanin miyar gargajiya da ta zamani.

1.1      Bitar ayyukan da suka gabata.

Abu ne da ya wajaba ga kowane irin bincike irin wannan ya yi waiwaye dangane da nazarce-nazarcen da aka gabatar a fagen bincike don ganin abin da masana da manazarta suka gudanar a fagen bincike, wato ko dai a xora a kan wata a qara wa Borno dawaki, hujjar ita ce ban samu wani aiki makammancin nawa ba. A wannan bincike nawa ba’a tsallake irin wannan tsari ba, don haka, na samu karanta wasu aikace aikacen da suka gabata kamar haka;

Murtala Maikuxi da Umaru Haruna Mayana 1989- 1990 Miyar gargajiya ta da da Hausawa ke yi, kundin digirin su na farko

9


wanda suka gabatar a Jami’ar Usmanu Xanfodiyo Sakkwato. Ni kuma aikin nawa yana Magana ne akan bambanci da kamamance tsakanin miyar gargajiya da ta zamani.

Calvin, Y. garba (1991) ya rubuta littafi mai suna Sana’oin Gargajiya a Qasar Hausa, marubucin ya yi qoqari qwarai da gaske wajen fito da nau’o’in sana’o’in Hausawa da yawa. To sai dai kasancewar sana’o’in da ya yi nazari na da yawa shi ya sa abin da nake ganin ya ce a sana’ar saqa da xunki bai taka rawar da ta karya kara ba. Sai dai marubucin ya yi qoqarin bayyana sana’o’in Hausawa da dama, idan aka yi la’akari da wannan aikin nawa za’a ga yana da bambanci da na shi aikin wato sun bambanta ta fuskar manufarsu.

Habibu Alhassan da Rubi’u, M. Zarruq (1982), sun rubuta littafi mai suna “Zaman Hausawa.” A wannan littafi sun yi qoqarin kawo nau’o’in sana’o’in Hausawa Su ma dai kamar C.Y. Garba ne sun gudanar da bincikensu ne a kan sana’o’in Hausawa, daban – daban, to amma ba su tava sana’ar abinci ba. Don haka wannan aikin nawa ya samu hurumin gudanar da shi.

10


1.2      Hujjar ci gaba da bincike

Idan aka yi la’akari da ayyukan da suka gabata da kuma matsayin wannan miyar ta gargajiya da ta zamani a al’ummar Hausawa sai a ce akwai bambanci tsakanin miyoyin guda biyu, kuma miyar zamani na neman mamaye ta gargajiya saboda abubuwan da zamani ya zo da su sababbi na haxa miya. Don haka in muka yi sakaci za mu tashi wata rana mu rasa samun kayan yin miyar gargajiya sai dai ta zamani. Don haka na yi qudurin wannan aiki ne domin tsokacin xan abin da ya samu na kawo bambanci da kuma kamance da a ke samu tsakanin miyar gargajiya da ta zamani, to amma iya binciken da na gudanar babu wani aiki da aka gudanar makamancin wannan aikin nawa. Saboda haka akwai buqatar ci gaba da gudanar da bincike musamman idan aka yi la’akari da yadda masu gidaje suke fuskantar barazanar zamani kan cefane da irin wahalar da marasa hali ke fuskanta wurin cefane, wasu suna wahala kafin su ciyar da iyalin su wannan shi ne hujjar ci gaba da bincikena.

11


1.3   Hanyoyin gudanar da bincike

A nan ne za’a yi bayanin yadda bincike zai gudana da kuma hanyoyin da za’a yi amfani da su domin samun bayanai da suka dace. Bayan haka kuma, na yi karance-karance a cikin littattafai da kuma kundaye da mujallu da kuma kafafen watsa labarai. Bugu da qari na yi qoqarin yin fira da mutane musamman tsofaffi waxanda ke yin sana’ar abinci akan yadda suke yin miyar su, wato waxanda suka ga jiya suka ga yau. Haka kuma na yi fira da matasa matan zamani a kan yadda suke yin miyoyin su na zamanin nan. Har ila yau na samu fira da manya-manyan mata masu sayar da abinci da kuma masu yin miyar buki, saboda suna da ra’ayi game da wannan binciken nawa sun nuna gamsuwarsu don babu wani aiki irin wannan ko kuma makamancin nawa. Suna ganin ni ne na farko da na tunkare su da irin wannan aiki na neme su ne don qarin bayani, don haka ina iya cewa masu gidajen abinci sun ba ni tasu irin gudunmuwa sosai.

1.4      MUHALLIN BINCIKE

Muhallin bincike shi ne wuri ko bagiren da aikin zai taqaita a kai, wato wurin da aikin zai tsaya a yayin gudanar da binciken. Don

12


haka, wannan binciken nawa ba zai tsallake garin Sakkwato ba. Idan aka ce garin Sakkwato to ana nufin unguwannin da ke cikin garin Sakkwato.

1.5   Muhimmancin Bincike

Babu shakka wannan aiki ne mai matuqar muhimmanci ta fuska daban-daban. Aikin zai cika givin da a ke da a wannan fannin ya kuma taka rawa wajen bunqasa ilimi baki xaya. Haka kuma zai iya zama wani abin amfani musamman ga manazarta na gaba masu shawar gudanar da bincike a wannan fanni.

Bugu da qari kuma aikin zai iya taka muhimmiyar rawa wajen bunqasa al’adun Hausawa da kuma wayar wa mutane kai idan an yi amfani da shi. Haka kuma aikin zai dubi irin rawar da miya ke takawa wajen ci gaban rayuwar Al’umma.

1.6   Naxewa

Wannan babin hoto ne na dukkanin aikin da za’a gabatar da kuma hanyoyin da za’a bi domin ganin aikin ya samu kammala cikin nasara. Ma’ana a wannan babi na yi gabatarwa a farko, sannan na duba ayyukan da suka gabaci wannan aiki da kuma hujjar ci gaba da bincike da mahimmancin binciken.


You either get what you want or your money back. T&C Apply







You can find more project topics easily, just search

Quick Project Topic Search