• The Complete Research Material is averagely 127 pages long and it is in Ms Word Format, it has 1-5 Chapters.
  • Major Attributes are Abstract, All Chapters, Figures, Appendix, References.
  • Study Level: BTech, BSc, BEng, BA, HND, ND or NCE.
  • Full Access Fee: ₦7,000

Get the complete project » Instant Download Active

Tsakure

Wannan bincike mai taken Raha a wasu Waqoqin Aliyu Namangi. Ya nazarci wasu waqoqin ne daga cikin waqoqin Aliyu Namangi waxanda ake hasashen cewa qunshe suke da zantuttuka na raha a cikinsu. Wannan bincike ya nuna cewa zantuttuka na raha na da matuqar muhimmanci a rayuwar al’umma musamman ma ga al’ummar Hausawa. Haka kuma binciken ya fahimci cewa wannan salo na yin amfani da zantuttukan raha a waqoqin Hausa kan haifar da nishaxuwa, da gundura yayin karantawa ko sauraron waqoqin. Sakamakon haka sai aka karkasa aikin zuwa babi-babi har guda biyar kamar haka: Babi na xaya ya kasance shimfixa ce da ke haskaka aikin baki xayansa. Babi na biyu kuwa ya waiwayi wasu ayyuka ne da suka gabata masu alaqa da wannan aikin. Babi na uku ya bayyana ire-iren hanyoyin da aka bi ne wajen tattaro bayanan da suka taimaka wajen gudanar da wannan binciken. A babi na huxu kuwa an bayyana wuraren da Aliyu Namangi ya sarrafa raha ce a wasu waqoqinsa. Wato kamar waqar Basukur da waqar zambon qazama da waqar Kuntugin Shaixan da waqar Tambihul Anami. Sai babi na biyar a inda aka naxe aikin gaba xayansa tare da bayar da wasu ‘yan shawarwari ga ‘yan uwa xalibai da kuma manazarta waqoqin Hausa.

Abstract

This research work titled “Raha a wasu waqoqin Aliyu Namangi” (Comedy in some of Aliyu Namangi’s poems) comprises of explanations of how the Artist used comedic expressions in some of his poems. The work also made some criticisms on the kinds of comedic statements he used in the poems to entertain the people. At the end of the study, it was discovered that Aliyu Namangi used these statements in his poems in order to strenghten the relationship that exists between him and his relatives even though the poems were spiritual in nature.

BABI NA XAYA SHIMFIXA

1.0    Gabatarwa

Marubuta waqoqin Hausa wasu mutane ne da Allah (S.W.T) ya ba su wata

baiwa da hikima da fasaha ga kuma basira wajen shirya waqoqin Hausa a rubuce,

domin isar da wasu saqonni masu muhimmanci ga al’umma. Haka kuma sukan

shirya waqa su kuma tsara ta a kan abubuwa daban-daban waxanda suka shafi

rayuwar jama’a.

Har wa yau kuma kusan kowanne marubuci da irin hanya ko salon da

yakan bi wajen tsara waqarsa, duk da cewa mafiya yawa daga marubuta waqoqin

Hausa sukan rubuta waqoqinsu ne bisa jigon wa’azi da gargaxi da tarbiyya ko

faxakarwa.

Haka kuma wani lokaci marubuta waqoqin Hausa kan yi amfani da wasu

zavavvun kalmomi ko wasu zantuka na musamman a waqoqinsu domin samar da

raha ko sanya nishaxi a zukatan jama’a saboda hakan zai haifar da rashin gundura

ga mai karatu ko sauraron waqoqin Aliyu Namangi.

Aliyu Namangi na xaya daga cikin ire-iren waxannan marubuta waqoqin

Hausa wanda ya yi amfani da wasu zavavvun zantuka na raha a wasu waqoqinsa,

a inda wannan bincike zai gudana a kansu domin gano ire-iren rahar da ya yi

amfani da su a waxannan waqoqin nasa da ake hasashen cewa suna qunshe da

zantuka na raha a cikinsu.

1.1       Taqaitaccen Tarihin Aliyu Namangi

Fagen nazari na tarihin rayuwa da ayyukan marubuta waqoqin Hausa, fage

ne mai faxi wanda masana da manazarta suka jima suna binciko tarihin xaixaikun


You either get what you want or your money back. T&C ApplyYou can find more project topics easily, just search

Quick Project Topic Search