SALON TALLATA „YAN TAKARA A WAQOQIN JAMHURIYA TA HUXU: NAZARI A KAN WASU WAQOQIN SIYASAR JAMHURIYA TA HUXU

SALON TALLATA „YAN TAKARA A WAQOQIN JAMHURIYA TA HUXU: NAZARI A KAN WASU WAQOQIN SIYASAR JAMHURIYA TA HUXU

  • The Complete Research Material is averagely 265 pages long and it is in Ms Word Format, it has 1-5 Chapters.
  • Major Attributes are Abstract, All Chapters, Figures, Appendix, References.
  • Study Level: BTech, BSc, BEng, BA, HND, ND or NCE.
  • Full Access Fee: ₦7,000

Get the complete project » Instant Download Active

TSAKURE

Siyasar Jamhuriya ta huxu a Nijeriya, ta zama tamkar kakar waqoqin siyasa. Saboda a wannan jamhuriya ce aka samu yaxuwa da bunqasar waqoqi da ake shiryawa ko dai a kan jam‟iyyu ko wasu xaixaikun „yan siyasa. A wannan lokacin ne aka samu waqoqi da jigogi iri daban-daban. Wasu game da aqidun siyasu ko „yan siyasa,wasu kuma masu nuna bijirewa ga jam‟iyyun siyasa ko shugabanni, wasu kuma ma xaixaikun „yan siyasa ne kawai suke wasawa. Wasu waqoqin ma duk da kasancewarsu na siyasa, ba su shafi jam‟iyya ba. Suna magana ne game da yanayin mulki da xabi‟un shugabanni. A wannan binciken an wasu waqoqin siyasa a jamhuriya ta huxu da suka zo da wani irin sauyi da aka samu na salon waqoqin, inda maimakon su mai da hankali ga yaxa manufofi da aqidun jam‟iyyu, sai suka karkata ga shirya waqoqi da suke wasa ko tallata xaixaikun „yan siyasa a cikinsu. Duk da cewa waqoqi ne na siyasa, amma wani lokaci, ko sunan jam‟iyyar da xan takarar ya ke ba a ambata. A wasu waqoqin ma, a cikin amshin ne kawai ake jin xuriyar sunan jam‟iyya. Kamar yadda Bahaushe ke cewa, „Ruwa ba ya tsami banza,‟ don haka ne a cikin aikin an gano wasu daga cikin dalilan da suka haifar da irin wannan salo waqoqin da ake shiryawa, musamman don tallata xan takaran ga jama‟a. A cikin babi na xaya an gabatar da aikin inda aka bayyana ginshiqan da aka shimfixa aikin a kan sa. Wato dalilin bincike da muhimmancin bincike da manufar bincike da farfajiyar bincike da hasashen bincike da hanyoyin bincike da sharuxxan bincike. Sannan kuma, an bayyana ra‟in bincike. A babi na biyu kuwa, an yi waiwaye adon tafiya, a inda aka duba ayyukan da suka gabata da suke da dangantaka da wannan aiki. An waiwayi ayyukan da suka yi magana a kan siyasar kanta, ko game da waqoqin siyasar wata jamhuriyya a keve ko a kan jam‟iyyun siyasa ko „yan siyasa da dai sauransu. Sannan kuma an duba taqaitaccen tarihin samuwar siyasa a Nijeriya da samuwar waqoqin siyasa da dalilan samuwar  salo ko           wasu jigogi a wannan jamhuriya(ta huxu). Haka kuma, an duba ire-iren jigogi da salon waqoqin siyasa. A babi na uku an yi sharhin wasu daga cikin waqoqin siyasa na jamhuriya ta huxu da aka xauka a matsayin misali daga jam‟iyyun ANPP da CPC da kuma PDP. Sai a babi na huxu aka duba salo da tsari na waxannan waqoqi. A babi na biyar an kammala bincike tare da bayyana abin da binciken ya gano domin tabbatar da hasashensa. Binciken ya gano wasu waqoqin siyasar Jamhuriya ta huxu da suka raja‟a a kan tallata xan takara kawai ba tallata aqida da manufofin jam‟iyya ba. Haka kuma mawaqan kan tallata „yan takara da fito da halayensu na kirki ta hanyar yabo da kirari.

ABSTRACT

Many political verses have emerged in the Fourth Republic in Nigeria. It is during this republic or political era that many poets composed poems of diversified themes; on parties‟ manifestos, aspirational candidate, party leaders and many more. There are, infact some other poems that are being composed to praise individuals only. Although these poems are political ones, hardly the names of the polical parties are mentioned in the poems. However, what predominates the poems superficially is the praise of the particular candidate, the poet is concerned with. Sometimes the party is only mentioned in the chorus. The findings of this research revealed the factors responsible for this type of poems. The chapter one of this work consists of problems, hyphothesis, objectives and scope and delimitation to the research. The theory of formalism and structuralism used for this research is also discussed in the chapter. The second chapter is made up of the literature review. The chapter three of this work contains analyses of the selected Hausa Political Verses in the Fourth Republic from ANNP, CPC and PDP. In chapter four, the style and structure of the selected poems have been analysed. Chapter five consists of the research findings and recommendations. The research has come out with new trend in Hausa Political Poetry, where the political poets, tilted toward the candidate not the party manifesto. It also discovered the new technique adopted by the Hausa political poets, in campaign composing poetry with full of simile and metaphors. The work has clearly discovered the departure of the contemporary Hausa poets and the traditional poets in the 60th and 90th.

BABI NA XAYA: SHIMFIXA

1.0 Gabatarwa

Siyasa wata aba ce da ta shafi rayuwar al‟umma a duniya, kuma ta yi tasiri matuqa a

zukatansu. Don haka ne ma mawaqan siyasa, su ma ba a bar su a baya ba, suke da irin

wannan tasirin a cikin jininsu da rayuwarsu ta yau da kullum. Saboda da wannan tasirin

ne, ya sa waqoqi na siyasa da kuma „yan siyasar kan su, sun zama tamkar jini da tsoka.

Watau dai, ba a raba su. Don haka ne ma ya sa waqa a qasar Hausa ba abin nema ba ce.

Domin kuwa, an yi nazarce-nazarce da dama a lokuta daban-daban a kan waqoqi, tun ba

na siyasa ba. Samuwar siyasa da havakarta a Nijeriya ya sanya ake samun waqoqi da ake

shiryawa kama tun daga masu yaxa manufofin jam‟iyyun siyasa da „yan siyasar kan su

da na yabon shugabannin siyasa da jam‟iyyunsu da na tallata siyasa da „yan takararsu.

Duk suna yin haka ne dangane da muhimmancin shiga jam‟iyya da kuma zaven

shugabanni na gari. Ganin yadda aka samu yawaitar waqoqi a wannan kakar siyasa a

jamhuriya ta huxu, ta kai ga yin la‟akari da cewa an sami waqoqi musamman da ake yi

wa „yan siyasa maimakon yi wa jam‟iyyu. A irin waxannan waqoqi ba manufofi da

aqidun siyasa ko jam‟iyya aka fi ba muhimmanci ba, babban abin da aka fi ba qarfi, shi

ne tallata xan takara. A wannan aiki an mai da hankali ne ga jigo da salon irin waxannan

waqoqi.

Wannan batu ne aka gudanar da bincike a kan sa, wanda ya shafi irin waqoqin da ake

shirya wa „yan siyasa domin bayyana su da kuma tallata su ga jama‟a kamar yadda aka

18


ambata a sama. Wannan shi ya sa aka gudanar da bincike game da waqoqi da suke tallata

„yan takara maimakon tallata aqidar siyasa. Daga qarshe an fahimci wani sabon salo da

masu shirya waqoqin Hausa suka xauka a fagen waqoqin siyasa.

Dangane da waqoqin siyasa kuwa, masana da dama sun bayar da ma‟ana daban-daban.

Birniwa, (1987 : 62 da 204) ya bayyana cewar Bello Gixaxawa ya bayyana waqar siaysa

da cewa:

“Ita ce waqar da ta qunshi cikakken yabo ga jam‟iyya da bayyana kyawawan manufofinta. Sannan kuma ta kasance ta kushe abokan gaba”.

Haka shi ma Yusuf Kantu, (Birniwa, 1987: 204 ) ya bayyana cewa :

“Waqar siyasa ita ce wadda ta qunshi kushe


You either get what you want or your money back. T&C ApplyYou can find more project topics easily, just search

Quick Project Topic Search