KEVAVVUN KALMOMIN INTANET DA AMFANINSU A NAZARIN HAUSA

KEVAVVUN KALMOMIN INTANET DA AMFANINSU A NAZARIN HAUSA

  • The Complete Research Material is averagely 146 pages long and it is in Ms Word Format, it has 1-5 Chapters.
  • Major Attributes are Abstract, All Chapters, Figures, Appendix, References.
  • Study Level: BTech, BSc, BEng, BA, HND, ND or NCE.
  • Full Access Fee: ₦6,000

Get the complete project » Instant Download Active

TSAKURE

Wannan aiki mai suna “Kevavvun Kalmomin Intanet Da Amfaninsu A Nazarin Hausa”, aiki ne da ya duqufa wajen samar da wani vangare na kevavvun kalmomin intanet na Hausa. Da farko, aikin ya yi qoqari wajen samar da kevavvun kalmomin intanet na Hausa ta hanyar fassara daga Ingilishi zuwa Hausa. An yi nazarin kevavvun kalmomin da aka samar qarqashin ilimin nahawun Hausa. Sannan aka yi gwajinsu a kan wasu muhimman hanyoyi waxanda ake ganin samuwar kevavvun kalmomin intanet na Hausa zai taimaka wa Hausa wajen amfani da intanet ba tare da bambancin ma’ana ba. Babbar manufar wannan aiki ita ce ba da ‘yar gudummuwa wajen bunqasa harkokin sadarwa na intanet a Hausa. Kodayake Hausawa sun daxe da qwarewa a sha’anin sadarwa ta yau da kullum, amma sha’anin intanet a yau ya riga ya shiga gaban kowace hanya ta sadarwa a wannan zamani. Saboda haka dole ne Hausawa su qara qoqari wajen koyon kwamfuta da amfani da intanet. A kan haka ne wannan bincike ya kammala da cewa Hausa tana da haske a sha’anin intanet, domin gudummuwar da masana suka bayar a vangaren hanyoyin sadarwa na kwamfuta sun nuna cewa Hausa tana da kyakkyawar safiya. Sai dai, matuqar ana son wannan harshe ya ci gaba da haskakawa, dole masana su taskace sababbin kalmomi na sha’anin kwamfuta da intanet da kuma sauran vangarorin da ci gaban zamani ya kawo. Sannan kuma Hausawa su shiga a dama da su a kowane vangare na amfani da kwamfuta da intanet; sannan masu hannu da shuni da ‘yan kasuwa su saka jari mai guivi a sha’anin sadarwa ta intanet.


You either get what you want or your money back. T&C Apply







You can find more project topics easily, just search

Quick Project Topic Search