NAZARIN JIGOGIN WA{O{IN SOYAYYA NA SADI SIDI SHARIFAI

NAZARIN JIGOGIN WA{O{IN SOYAYYA NA SADI SIDI SHARIFAI

  • The Complete Research Material is averagely 80 pages long and it is in Ms Word Format, it has 1-5 Chapters.
  • Major Attributes are Abstract, All Chapters, Figures, Appendix, References.
  • Study Level: BTech, BSc, BEng, BA, HND, ND or NCE.
  • Full Access Fee: ₦6,000

Get the complete project » Instant Download Active

Babi Na [aya

Shimfi]a

1.0.   Gabatarwa

A }alla akwai fannoni uku manya na nazari a harshen Hausa. Fannonin su ne abin da ya shafi ilimin kimiyar harshe, da adabi, da kuma fannin al’adu. Abin da za a yi aiki a kansa yana }ar}ashin fannin adabi ne, wato wa}a. Wa}a ta kasu zuwa gida biyu, rubutacciya da ta baka. Rubutacciyar wa}a ta samu ne bayan Bahaushe ya iya karatu da rubutu, amma wa}ar baka ta ]a]e da samuwa wato ta jima a cikin adabin Bahause.

Akwai ire – ire na wa}o}in baka da dama, wa]anda suka ha]a da, Wa}o}in mata, da wa}o}in ban dariya da kuma, wa}o}in soyayya. A

kan wa}o}in Soyayya za a gudanar da wannan bincike, a inda za a ra~e cikin wa}o}in Sadi Sidi Sharifai na Soyayya, wa]anda suke na baka ne.

1.1.     DALILIN BINCIKE

Dalilin yin wannan bincike shi ne taskace wa}o}in wannan fasihi (Sidi Sharifai) da Jigojinsu da kuma salailansu . Sannan kuma za a gudanar da

10


wannan bincike ne don samun digiri na farko a sashin harsunan Najeriya.

Jami’ar Usman [anfodiyo, Sokkwato.

1. 2.  MANUFAR BINCIKE

\Soyayya kamar yadda aka sani, wani jigo ne a cikin adabin Hausa, domin haka yana daga cikin manufar wannan bincike, }ara ha~aka wannan jigo na Soyayya, sakamakon yawa da ba shi da shi a cikin adabin Hausa, wannan ne ma ya sa aka ]auki wa}o}in Soyayya na Sadi Sidi Sharifai don a taskance.

I. 3.   MATSALOLIN BINCIKE

Babu Shakka akwai gi~i a cikin adabi da ya kamata a cike. Wannan gi~i shi ne na wa}o}in Soyayya. Saboda ba a fiye a nazarinsu ba. Har ma wasu na tunanin ko Hausa ba ta da wannan jigo (na Soyayya) to wannan ne ya sa aka ]auki wa}o}in Soyayya na Sadi Sidi Sharifai a yi aiki a kansu.

1. 4.  FARFAJIYAR BINCIKE

Duk da cewa wannan aiki zai gudana a harshen Hausa, kuma fannin adabi, adabin ma a wa}ar baka ta soyayya. A cikin wa}o}in soyayyar ma ba kowanne ba, za ayi nazarin wa}o}in soyayya na Sadi Sidi Sharifai zalla.

1. 5.    HUJJAR CI GABA DA BINCIKE

11


Za a ci gaba da wannan bincike ne, Sakamakon ba wani aiki da aka ta~a samu akan wannan fasihi, duk da cewa an yi aiki a kan wa}o}in Soyayya da dama, amma ba a yi a kan Sadi Sidi Sharifai ba.

1. 6.  HANYOYIN GUDANAR DA BINCIKE

Hanyoyin da aka bi don gudanar da wannan bincike su ne:-

Ganawar da aka yi da Sadi Sidi Sharifai ido da ido, ranar 21 ga watan 6 Shekarar ta 2015 a gidansa da ke anguwar Sharifai. Sa’annan kuma an gana da shi a Situdiyonsa da ke kan titin Zoo Road, Ranar 11 ga watan 7 shekara ta 2015.

An ziyarci dakin dakin karatu na Murtala Muhammad da ke Kano. Kuma an samu shawarwari daga malaman da ke sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu [anfodiyo, Sakkwato.

1. 7.  BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA

Hausawa na cewa “waiwaye adon tafiya” duk aikin da za a yi, ya kamata a yi bitar ayyukan masana da manazarta da suke da ala}a da wannan aiki ko suka yi kama da shi, da nuna hanyar da za su sha bamban da juna da

12


wannan aiki. An nazarci kundaye, da ma}alu da kuma littattafai. Ayyukan da aka nazarta wa]anda ke da nasaba da wannan aiki su ne:-

Ashiru (2001) kundin digiri na farko mai taken: “Jigon kishi a cikin rubutattun wa}o}in Soyayya” wannan kundi ya yi tsokaci kan kishi da abin da ke haifar da kishi, tsakanin namiji da mace.

Wannan aiki yana da ala}a da nawa domin kishi jigo ne a cikin jigogin soyayya. Bayan haka kuma a wa}o}in soyayya da za ayi nazari akwai jigon kishi, amma wa}o}in wandanda Sadi Sidi Sharifai ya yi ne. Saboda haka wannan aiki ya sha bamban da nawa.

Bello, (2004) a Kundinsa na neman digirin farko mai taken: “Tasirin zamani kan soyayya” a wannan aiki ya kawo ma’anar so da kuma kashe – kashensa. Bayan wannan kuma ya yi bayani kan yadda soyayya take jiya da yau, haka kuma aikin ya yi bayani game da illolin soyayya. Wannan aiki ya sha bambam da nawa, don ni zan yi aiki kan Sadi Sidi Sharifai ne da wa}o}insa na soyayya.

Muhammad. (2010) kundi mai taken “Kalaman cikin wa}o}in soyayya, gaskiya ko ru]i" An yi wannan aiki ne don neman digirin farko a sashen koyar da Harsunan Nigeriya Jami’ar Usmanu [anfodiyo Sakkwato. A

13


cikin wannan aikin an yi }o}arin bayyana irin rawar da marubuta da masu rera wa}o}in soyayya na Hausa ke takawa, musamman wajen salo a cikin wa}o}in. Shi ma wannan aiki yana da ala}a da nawa tunda a kan wakokin soyayya ya gudana. Amma ni nawa ya sha bamban da shi, saboda a kan wakokin soyayya na Sadi Sidi Sharifai zan yi shi.

Lawal, (2014) a kundinsa na neman digiri na farko a Jami’ar Usmanu [anfodiyo Sakkwato, mai taken “Salon Sarrafa harshe a cikin }agaggun Labaran Hausa”. Nazari daga litafin Za~i-naka, a cikin aikin ya yi ba yanin salo da sarrafa harshe, da wannan marubuci ya kawo filla – filla. Wannan aiki yana da ala}a da nawa amma ta fuskar salo da sarrafa harshe kawai. Ni kuma nawa, zai kalli salo da sarrafa harshe amma a cikin wa}o}in soyayya na Sadi Sidi Sharifai.

Umar, (2011) a cikin kundinsa na neman digirin farko a sashen Harsunan Nigeriya Jami’ar Usmanu [anfodiyo Sakkwato, mai taken “Salo da Sarrafa harshe a cikin wa}o}in Ibrahim Aminu [andaso, na Aliyu magatakarda Wamakko. A cikin wannan aiki, an yi }o}arin fito da salailai daban – daban da ma’anar Salo da mahimmancinsa da Sauransu.

14


Shi ma wannan aiki yana da ala}a da nawa ta fuskar salo kawai duk da cewa shima a kan wa}o}in wani ya yi. Ni kuma a kan wakokin soyayya na Sadi Sidi Sharifai nawa aikin zai gudana, inda za a kalli jigoginsu da salailansu.

Hamza, (2011) a kundinsa na neman digirin farko a sashen koyar da Harsunan Nigeriya Jami’ar Usmanu [anfodiyo Sakkwato, mai taken Salo da sarrafa harshe a wa}o}in Aminuddeen Ladan Abubakar (ALA). Aikin ya bayyana Salo da ire – irensa duk a cikin wa}o}in Ala. Shi ma wannan yayi tarayya da nawa aikin ta fuskar salo, sai dai shi wannan a kan wakokin ALA ya gudana, ni kuma nawa a kan wakokin soyayya na Sadi Sidi Sharifai zai gudana.

Malumfashi, (2000) a ma}alarsa mai taken “Makomar Adabin Kasuwar kano.” A cikin mu}alar ya yi bayanin tarihin samuwar rubutun Zube, ya }ara sa bayanin ire – iren Littatafan farko na Soyayya, kuma ya yi bayanin hada sashen da kamfanin NNPC Zariya yayi a shekarar 1978.

Wannan takarda tana da ala}a da aikina tunda ta tabo abunda ya shafi soyyaya amma cikin littattafan zube, ni kuma a kan wa}o}in soyayya na Sadi Sidi Sharifai aikina zai gudana.

15


Yahya, (2001) a cikin littafinsa mai suna “Salo Asirin Wa}a” a ciki ya yi bayanin ma’anar salo a cikin wa}a. Sannan kuma ya bayyana muhimmancin salo, bayan wannan kuma ya yi bayani akan sauran dabarun sarrafa harshe kamar, Jinsarwa, kamance, kinaya, zayyana da makamantansu. Wannan aiki na da dangantaka da nawa, sakamakon salo da za a kalla a cikin wa}o}in soyayya na Sadi Sidi Sharifai da kuma kawo ma’anar shi salon.

Sa’id (1982) a Littafinsa mai suna “Dausayin Soyayya”. Wannan Littafi ya yi }o}arin ya tattara rubutattun wa}o}i na Soyayya, sai dai bai yi sharhi a kan su ba. Shi ma wannan aiki yana da ala}a da nawa duk da cewa shi wa}o}in soyayya ya taskace rubutattu da na baka, ni kuma a kan wa}o}in soyayya na Sadi Sidi Sharifai zai gudana.

Bunza, (2009) a Lttafinsa mai suna “Naramba]a” ya kawo tarihin Naramba]a da wa}o}insa, da fito da ma’anar Salo da ire – irensa. Da sauran abubuwan da ake iya samu cikin wa}a. Wannan aiki yana da ala}a da nawa duk da cewa kan Naramba]a aka yi shi, amma tun da an kalli salo da ma’anarsa to yana da ala}a da nawa sai dai ni a kan wa}o}in soyayya na Sadi Sidi Sharifai aikina zai gudana.

16


Bisa la’akari da ayyukan da suka gabata, na kundaye har zuwa littattafai, za a samu cewa ba wani aiki da ya yi daidai da nawa, saboda an yi wasu ayyuka akan wasu mawa}a daban, ko ma a kan wani abu da ya shafi Soyayya.


You either get what you want or your money back. T&C Apply







You can find more project topics easily, just search

Quick Project Topic Search